18 Nuwamba 2021 - 11:33
​Iran: Kudurin Hukumar Kare Hakkin Bil'adama Mai Lamba L. 28 Kira Ce Ga Kiyayya Da Iran

Zahra Ershadi, mataimakiyar jakadan kasar Iran a MDD ta bayyana kudurin da hukumar kare hakkin bil’adama da MDD ta fitar a ranar Laraba 17 ga watan Nuwamba da muke ciki dangane da abinda suka kira ‘yanayin kare hakkin bil’adama a kasar Iran” a gaban kwamiti na 3 na majalisar ya na dai dai da kira ga kasashen duniya su ki kasar Iranne.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Zahra Ershadi tana fadar haka a gaban kwamiti na 3 na kwamkin tsaro a jiya Laraba, ta kuma kara da cewa, ganin Irin kasashen da suka gabatar da bukatar a samar da wannan kuduri don bata sunan Iran a duniya, wato kasashen Canada, Amurka da Isra’ila da sauran kasashen yamma, ba abin mamaki bane.

Don wadanan kasashe su ne a gaba a duniya wajen kashe yara kanana a kasar Falasdinu da suka mamaye, ko kuma kasar Canada inda aka yi wa yara kanana ‘yan makarantar kwana ‘yan asalin kasar piyade, sannan a kashe su a binne a kaburbura na gama gari.

Don haka Iran bata amince da wannan kudurin ba, don siyasa ce aka sanay ciki ba gaskiyan abinda yake kasa ba ne.

Banda haka Ershadi ta kammala da cewa kasar Iran tana bakarta na mutunta dukkan kudurrin kasa da kasa da suka shafi kare hakkin bil’adama.

342/